Sojojin ƙasar Amurka sun tsara wasu shirye-shiryen kai farmaki a Najeriya bisa umarnin shugaban ƙasar, Donald Trump, domin kare Kiristoci daga hare-haren ‘yan ta’adda, kamar yadda jaridar The New York Times ta ruwaito a ranar Alhamis.
A cewar jaridar Times, jami’ai sun ce da wuya sojojin Amurka su iya kawo karshen tada kayar bayan da aka kwashe shekaru aru-aru ana yi a Najeriya duk da umarnin Trump, inda suka ce sai an gudanar da yaƙi irin na Iraq ko Afghanistan kafin a sami nasara.
Shirin da rundunar sojin Afirka ta Amurka (AFRICOM) ta gabatar ya ƙunshi matakai uku da ya haɗar da ƙarami, matsakaici, da kuma babba, waɗanda ke bayyana matakan shiga lamarin.
An mika waɗannan shawarwari ga ma’aikatar tsaron ƙasar Amurka bayan da shugaban Trump ya yi barazanar kai farmaki domin dakatar da abin da ya kira “hari kan Kiristoci masu daraja.”
A karkashin shirin ƙarami, AFRICOM ta ba da shawarar haɗin gwiwa da sojojin Najeriya wajen kai farmaki kan mayakan Boko Haram da kuma ISWAP, inda Amurka za ta ba da bayanan leƙen asiri da tallafin dabarun yaƙi.
Sai dai wannan shirin ba zai haɗa da hukumar raya ƙasashe ta Amurka (USAID) ba, wadda ta rufe ofishinta a birnin Abuja tun a watan Yuli, bayan umarnin da gwamnatin Trump ta bayar.
Jaridar The New York Times ta ce shirin matsakaici ya haɗa da amfani da jiragen yaki marasa matuƙa wajen kai hari kan sansanonin ‘yan ta’adda a arewacin Najeriya, amma ana fuskantar cikas saboda Amurka ta rufe sansanoninta na jiragen yaki a ƙasar Nijar a watan Agusta, waɗanda yanzu ke ƙarƙashin ikon Rasha.
Shirin mafi girma kuma ya haɗa da tura jirgin yaƙin ruwa na Amurka zuwa Tekun Guinea domin kai hare-hare daga nesa cikin arewacin Najeriya, sai dai rahoton ya nuna cewa wannan mataki ba a ɗauke shi a matsayin fifikon tsaron ƙasa na shekarar 2025 ba.
Wasu manyan jami’an soji sun bayyana cewa wannan rikici ba zai warware ta hanyar yaƙi kaɗai ba, saboda yana da nasaba da rikice-rikicen ƙasa, kabilanci, da tattalin arziki.
Haka kuma Boko Haram da ISWAP sun dade suna kai hare-hare kan Kiristoci da Musulmai, suna amfani da rashin daidaito tsakanin al’umma don faɗaɗa tasirinsu.
Gwamnatin tarayya ta Najeriya ta musanta bayanan da ke nuna cewa ana nuna rashin adalci ga Kiristoci, inda shugaban ƙasa Bola Tinubu ya jaddada cewa Najeriya ƙasa ce mai bin tsarin mulki da ke tabbatar da ‘yancin addini, kuma gwamnati tana ci gaba da tattaunawa da shugabannin addinai domin warware matsalolin tsaro.
Duk da haka, rahoton The New York Times ya jaddada cewa gwamnatin Najeriya ta nace cewa duk wani shirin waje da zai shafi ƙasar “ya zama cikin girmama ikon ƙasa da cikakken ‘yancin Najeriya.”













































