Shugabar mata a jam’iyyar NNPP ta yi murabus

Aisha Ahmad Kaita, shugabar, mata, jam'iyyar, NNPP, murabus
Shugabar Mata ta shiyyar Arewa maso Yamma na Sabuwar Jam’iyyar NNPP Hajiya Aisha Ahmed Kaita ta yi murabus daga mukaminta.Jaridar SOLACEBASE ta rawaito cewa...

Shugabar Mata ta shiyyar Arewa maso Yamma na Sabuwar Jam’iyyar NNPP Hajiya Aisha Ahmed Kaita ta yi murabus daga mukaminta.

Jaridar SOLACEBASE ta rawaito cewa Kaita ta sanar da murabus din na ta ne a wani taron manema labarai a ranar Talata a Kano.

Ta ce ta yi murabus daga mukamin na ta ne na son rai amma duk da haka, ta ci gaba da zama a jam’iyyar.

Karin labari: ‘Yan bindiga sun kai hari masallaci tare da awon gaba da wasu a jihar Zamfara

Akan dalilanta na murabus, Hajiya A’isha Kaita ta ce ya zama wajibi ta yi murabus domin tun kafa gwamnatin NNPP a Kano mabiyanta da suka goyi bayan nasarar zaben da gwamnatin ta samu ba’a tafiyar da su ta fuskar nadawa ko tuntuba.

“A jiya na sanar da shugaban jam’iyyar NNPP da Kwankwasiyya na kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso kudirina na sauka daga mukamina na shugabar mata na shiyyar Arewa maso Yamma, ya tambaye ni ko akwai matsala a kan mataki na amma na ce ina son dai na ajiye ne.

Karin labari: Ranar Wayar Da Kai Kan Cutar Autism ta Duniya: Tinubu Ta Nemi Lalubo Hanyoyin Tallafawa Masu Cutar

Har yanzu ni memba ce a jam’iyyar amma ina bukatar in sauka daga mukamin shugabar mata na shiyyar” Aisha ta shaida wa manema labarai.

“Ni babban mai goyon bayan Rabi’u Musa Kwankwaso ce kuma ina tare da shi a APC da PDP har izuwa NNPP.’’

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here