Ranar Wayar Da Kai Kan Cutar Autism ta Duniya: Tinubu Ta Nemi Lalubo Hanyoyin Tallafawa Masu Cutar.

FB IMG 17120547143840924

Uwargidan shugaban kasa, Sen. Oluremi Tinubu, ta ce gano cutar gaulanci tunda wuri-wuri wato Autism zai iya taimaka wa mutanen da ke fama da cutar a samu gaggarumin nasara.

Hakan na kunshe ne a cikin sakon da uwargidan shugaban kasar ta aike kan ranar wayar da kan jama’a ta duniya kan cutar gaulanci wato Autism, wadda ake yi a kowacce shekara a ranar 2 ga Afrilu.

Rayuwa da iyalai tare da ƙaunar na iya zama ƙalubale. A yau, ina jinjina tare da nuna farin ciki da soyayya domin sadaukarwa ga masu irin wannan cuta.

“Na kuma fahimci rawar da ƙungiyoyin al’umma ke takawa wajen samar da tallafi da dama ga mutanen da ke fama da irin wannan cuta da iyalansu. Duk da haka, ganewar cutar tun asali da kuma maida hankali kanta suna da mahimmanci don tabbatar da mutanen da ke da cutar sun kai ga samun cikakkiyar lafiya.

“Ina kira ga iyaye da masu kulawa da su mai da hankali kuma su nemi taimakon kwararru a duk lokacin da wata damuwa ta taso.”

Ta kuma yi kira da a kara nuna kauna da goyon baya ga kowa a cikin al’umma domin shawo kan wannan kalubale ga masu fama da irin wannan cuta.

“Za mu iya samar da wani yananyi duniya inda daidaikun mutane ba tare da la’akari da su wanene su ba da kowanne irin ƙalubalen da suke fuskanta a rayuwa, ana ƙarfafa musu gwiwa, domin hakan ya basu dama jin ba a ware su ba,” in ji ta.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi kiyasin cewa kusan daya cikin yara 160 a duk duniya na cikin yanayin cuta. A Najeriya, an kiyasta cewa cikin yara 88 akwai guda 1 dake fama da wannan cuta, a cewar WHO.

Duk da haka, WHO ta ce yawancin lokuta ba a iya gano irin wannan yanayi da wuri, Hukumar lafiya ta duniya ta kuma ce a duk duniya, an kiyasta cewa kusan kashi 31 cikin 100 na mutanen da ke da cutar suma suna da nakasa ta hankali.

Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 2 ga Afrilu a matsayin ranar wayar da kan jama’a game da cutar Autism ta duniya a shekara ta 2007. Majalisar Dinkin Duniya tana karfafa kasashe mambobin kungiyar da su dauki matakan wayar da kan jama’a game da masu cutar a duk fadin duniya.

Wannan rana daya ce daga cikin ranaku bakwai na musamman na Majalisar Dinkin Duniya na musamman na kiwon lafiya. Bikin na 2024 a karon farko zai nemi ba da cikakken bayani game da halin da al’amura dakuma jin halin da masu fama da wannan cuta ke ciki a duniya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here