Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da umarnin rufe wurin hakar zinare na Mararrabar Birnin Yauri da ke karamar hukumar Ngaski, bayan samun rahoton tashin hankali tsakanin al’ummomin yankin da wakilan gwamnatin tarayya.
Idris ya yi wannan umarni ne a yayin ziyarar bazata da ya kai wurin a ranar Alhamis, inda ya ce jami’an tsaro su mamaye wurin har sai an cimma matsaya tsakanin gwamnatin jihar da shirin gwamnatin tarayya na kawo tsari da inganta harkar haƙar Zinare (PAGMI).
Gwamnan ya bayyana cewa dole ne a tabbatar da cewa al’ummomin da ke da gonakin kasa inda ake hakar ma’adinai sun amfana.
Ya ce duk da cewa gwamnati ba ta ci gajiyar hakar ma’adinai kai tsaye, mutanen yankin da kasa take yasu dole ne su samu kulawa ta musamman.
Haka kuma, ya ba da umarnin ga ma’aikatar hakar ma’adinai ta jihar da ta tattara cikakken bayanan dukkan kamfanoni, kungiyoyi da mutane da ke da lasisin hakar ma’adinai a Kebbi domin kawo tsari da tsafta.
Labari mai alaƙa: Ƙaramar hukumar Yauri ta sanya dokar hana fita biyo bayan rikicin masu haƙar ma’adinai ya yi sanadiyyar mutuwar mutane
Idris ya tunatar da cewa an taba samun rikici sakamakon hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, inda aka rasa rai a kwanan nan a yankin.
Ya ce gwamnati ba za ta yarda da wannan hali ba, musamman ganin cewa wasu daga kasashen waje irin su Mali, Chadi, Nijar da Tanzaniya na shiga su haddasa barazanar tsaro.
Gwamnan ya kuma bayar da umarnin a saki kusan matasa 50 da aka tsare saboda rikicin hakar zinaren, ta hanyar sulhu ba tare da ci gaba da shari’a ba.
A nasa jawabin, wakilin PAGMI, Musa Adamu-Dantata, tare da kwamishinan haƙar ma’adinai na jihar, Garba Hassan-Warrah, sun yi wa gwamnan bayani kan koke-koke da matsalolin da ake fuskanta a wurin haƙar zinaren.
NAN













































