Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana damuwa kan abin da ta kira yawaitar amfani da umarnin kotu wajen neman mallakar dukiyar jama’a, tana gargadin cewa wannan yanayi na barazana ne ga adalci, zaman lafiyar jama’a, da muradun jama’a baki daya.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya yi wannan gargadin a taron “Makon Shari’a” da Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA), reshen Ungogo, ta gudanar a Kano, inda Kwamishinan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Jihar, Abdulkarim Kabiru Maude, SAN, ya wakilta shi.
Gwamnan ya nuna damuwarsa cewa mutane na kara samun umarnin kotu domin neman mallakar kadarori kamar makarantu, asibitoci, makabarta, da sauran wuraren jama’a, wanda hakan kan kawo cikas ga amfani da al’umma ke yi da su tun da dadewa.
“Hukunce-hukuncen kotu kan irin wadannan abubuwan sun fi karkata wajen kare muradun mutum daya fiye da jin dadin al’umma, ainihin ma’anar adalci na raguwa,” in ji shi.
Ya ce a wasu lokuta, masu neman mallaka na samun umarnin hana amfani da wurin cikin dan gajeren lokaci, wanda hakan ke hana al’umma kusantar kadarorin da suka dade suna amfanar su.
Yayin da ya sake jaddada muhimancin girmama kotu, gwamnan ya yi gargadi cewa irin wadannan abubuwa, idan ba a dakatar da su ba, na iya sa jama’a su rage amincewa da tsarin shari’a da tsaro.
Gargadin ya zo ne a daidai lokacin da ake samun kara damuwa kan ƙalubalen tsaro da ke tasowa a jihar da ma fadin arewacin Najeriya, wanda ya ce suna da sarkakiya kuma suna da alaƙa da juna, galibi abubuwan zamantakewa da tattalin arziki ne ke haddasa su.











































