Tsohon shugaban hukumar ma’aikatan majalisar dokoki Adamu Fika ya rasu

Fika 750x430

Tsohon Shugaban hukumar ma’aikatan majalisar Dokoki ta Kasa (NASC), Dr. Adamu Mohammed Fika, ya rasu yana da shekaru 84.

Sanarwar ta fito daga Alhaji Mohammed Abubakar (Chokalin Fika), na Mataimaki na Musamman kan Harkokin Yada Labarai ga Mai Martaba Sarkin Fika, Alhaji Dr. Muhammad Ibn Abali Muhammadu Idrisa.

Sanarwar ta ce za a gudanar da sallar janazar marigayin a ranar Juma’a, 7 ga watan Agusta, a Masallacin Kasa da ke Abuja.

Sanarwar ta ce Fika, wanda ke da sarautar gargajiya ta Zarma Kura a Fika, ya rasu a wani asibiti a Abuja.

Marigayi Fika shi ne Darakta Janar na farko kuma Babban Magatakardar Majalisar Dokoki ta Kasa, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa tsarin gudanarwa na majalisar dokokin kasa a farkon Jamhuriya ta Hudu a shekarar 1999.

Daga baya ya yi aiki a matsayin Shugaban Hukumar Ma’aikatan Majalisar Dokoki ta Kasa – NASC, inda ya ba da gudummawa wajen karfafa gudanarwa da sarrafa Majalisar Dokoki ta Kasa.

Har zuwa rasuwarsa, shi ne Shugaban Kwamitin Aminttu na Majalisar Manyan Magatakardu da Sakatarorin Majalisar Dokoki masu Ritaya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here