NLC DA TUC sun nemi Naira 500,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi ga ma’aikata

NLC joe ajaero

Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC0 da ta ‘Yan Kasuwanci (TUC), sun bukaci Gwamnatin Tarayya ta biya ma’aikatan Najeriya sabon mafi karancin albashi na naira dubu dari biyar 500,000.

Mataimakin Shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa kuma Shugaban Kungiyar Malamai (NUT), Kwamred Audu Titus Amba, ne ya gabatar da wannan bukata a taron tattaunawa kan Hakkokin Ma’aikatan Najeriya da aka gudanar a ranar Alhamis a Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi.

Kwamred Amba, wanda ya wakilci Shugaban NLC, Kwamred Joe Ajaero, ya ce wa’adin karin albashin naira dubu saba’in 70,000 da aka tattauna tsakanin kungiyar kwadago da gwamnatin tarayya ya kare a watan Yuli.

“Don haka muna so mu shiga wata sabuwar tattaunawa da gwamnatin tarayya mu nemi a biya ma’aikatan kasar nan akalla Naira 500,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi,” in ji Amba.

Ya jaddada cewa, a halin da ake ciki yanzu, duk wani karamin albashi da ya gaza Naira 500,000 ba zai biya bukatun ma’aikata ba saboda wahalar rayuwa da talauci da ke fuskantar ma’aikatan gwamnati a kasar.

Shugaban NLC ya ce, duk da haka, kungiyoyin ba sa adawa da gwamnatin tarayya, abin da suke so shi ne su daidaita don sabuwar tattaunawa kan sake duba mafi karancin albashi bisa la’akari da halin da ma’aikata ke ciki.

Kwamred Amba ya yaba wa Gwamna Nasir Idris bisa samar da yanayi mai kyau don gudanar da taron, wanda ya samu halartar wakilai kusan 1,000.

Ya kara da cewa mahalarta taron sun tattauna matsalolin da ke shafar ma’aikata da shugabancin kungiyoyin kwadago a fadin kasar domin samar da mafita.

A nasa bangaren, Kwamred Nuhu Toro, wanda ya wakilci Shugaban TUC na kasa, ya ce ma’aikatan Najeriya suna bukatar aiki na gaskiya ba alkawari ba, inda ya jaddada cewa samun albashin da zai iya biyan bukatu yana da matukar muhimmanci wajen inganta rayuwarsu.

Ya yi kira ga gwamnatoci a kowane mataki da su kawo karshen daukar ma’aikata na wucin gadi, ya ce samun aikin dindindin zai kara yawan aiki da kuma inganta ci gaban tattalin arziki.

“Ma’aikatan Najeriya suna bukatar aiki, ba magana ba. Samun albashin da zai iya biyan bukatu shi ne hanyar tabbatuwa ga tattalin arziki na adalci,”in ji shi.

Da yake bude taron, Gwamna Nasir Idris ya tunatar da kungiyar cewa shi ne gwamna na farko da ya aiwatar da mafi karancin albashi na Naira 75,000 ga ma’aikatansa a kasar nan.

Ya yi alkawarin zai isar da sabbin bukatun kungiyoyin a daya daga cikin tarukan kungiyar gwamnoni.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here