Babban Bankin ƙasa CBN ya karyata rahoton da ke cewa ya ware dala biliyan 1.269 domin shigo da kayayyakin mai a watanni uku na farkon shekarar nan.
A cikin wata sanarwa da bankin ya fitar a ranar Talata, ya bayyana cewa rahoton da ke yawo a kafafen labarai ya saɓa da gaskiya kuma ba daidai ba ne.
Bankin ya ce wasu rahotanni sun yi kuskuren nuna cewa ya raba dala biliyan 1.259 ga manyan kamfanonin mai don shigo da man fetur da sauran kayayyakin da suka shafi harkar mai.
Ya bayyana cewa wannan bayani ba gaskiya ba ne, domin babu wani ware kudade da aka yi domin shigo da man fetur a cikin lokacin da aka ambata.
CBN ya tabbatar da cewa yana ci gaba da gudanar da ayyukansa bisa gaskiya da tsari wajen kula da harkokin musayar kuɗaɗe da tattalin arzikin ƙasa.
Bankin ya kuma bukaci kafafen yada labarai da su tabbatar da sahihancin bayanai kafin wallafawa don gujewa yada rahotanni marasa tushe.













































