Na yi aiki da tsoron Allah, a shirye nake in ba da bayanan ayyuka na – Mele Kyari

mele kyari NNPC Boss 750x430

Tsohon Shugaban rukunin kamfanin Mai na Najeriya (NNPC) Mele Kyari, ya musanta cewa yana hannun hukumar yaki da masu yi wa tattalin Arzikin kasa tu’annati (EFCC).

Yayin da yake mayar da martani ga rahoton cewa yana tsare a hannun hukumar ta EFCC, Kyari ya ce ya sha samun kiraye-kiraye daga bangarori daban-daban kan labarin karyar da ake yadawa.

Ya ce ya bauta wa Najeriya da tsoron Allah kuma a shirye yake a yi masa hisabi a kan shugabancinsa.

“A cikin ‘yan kwanakin da suka gabata musamman a cikin sa’o’i biyu da suka wuce, na yi ta fama da kiraye-kirayen ‘yan uwa da abokan arziki kan ikirarin da wata jarida ta intanet ta yi cewa ina hannun hukumar yaki da yi wa tattalin Arziki tu’annati (EFCC).”

“A halin yanzu, ina hutun da ya dace bayan rushe shugabancin mu da hukumar ta NNPC ta yi”.

Dole ne in jaddada cewa na yi aiki da tsoron Allah, na sani sarai, a matsayina na musulmi, cewa idan ban yi lissafi a gaban mutum ba, to lalle zan yi hisabi a gaban Allah, na fi dacewa da lissafin ma’aikatun dan Adam, saboda haka, da na yi hidima a matsayin ciyar da jama’a gaba.”

Karin karatu: Hukumar NDLEA ta kama wasu abubuwan fashewa 942 a jihar Zamfara

“A kan haka ne nake kira ga kafafen yada labarai da su rika bin diddigi tare da kaucewa yada karya wajen yaudarar jama’a da labaran da ba a tabbatar da su ba ko kuma wasu batutuwa da ke bukatar karin tabbaci daga hukumomin da abin ya shafa.”

“Ina godiya kwarai da gaske ‘yan uwa da abokan arziki da suka tuntube ni, kuma ina tabbatar musu da cewa a shirye nake in amsa duk wata tambaya da za a yi mun,” in ji shi.

A ranar 2 ga Afrilu, Tinubu ya cire Kyari saboda bukatar samar da ingantaccen aiki, maido da kwarin gwiwar masu saka hannun jari, da kuma kamfanin NNPC na kasuwanci”.

A wani bangare na garambawul, shugaban ya nada Bayo Ojulari a matsayin sabon shugaban kamfanin, sannan Ahmadu Musa Kida a matsayin sabon shugaban kamfanin mai na NNPC wanda ya maye gurbin Pius Akinyelure.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here