Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Rigasa, Kaduna ta bayar da umarnin a tsare wata mata da wayar ta ta yi kara a lokacin da ake gudanar da shari’ar.
A zaman kotun na ranar Talata, Alkalin kotun, Malam Muhammad Adamu, ya ce za a tuhume ta ne da laifin kawo cikas ga shari’ar kotun.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa wayar matar da take yin kallo a kotun ta yi kara a yayin da ake ci gaba da shari’a kuma ta ki mika wayarta ga jami’in kotun, lokacin da aka bukaci ta yi hakan.
Ta ce wannan ne karon farko da ta shiga kotu, inda ta kara da cewa tana son ta ga yadda ake shari’a a kotun.
Karanta: a Hajj 2025: NAHCON da hukumar jin dadin alhazai ta jiha sun tsayar da ranar fara jigilar Maniyyata.
Duk da rokon da ta yi, an kama matar da ba a bayyana sunanta ba, kuma an kama wayarta.
NAN ta ruwaito cewa an sanya wata alama da ke nuna cewa a kashe wayoyi a bangon waje da kuma cikin harabar kotun.
Har ila yau, ma’aikacin kotu ya sanar da cewa a kashe wayoyi ko kuma a sanya ta ta yi shiru kafin a fara shari’ar kotun.(NAN)










































