Hajj 2025: NAHCON da hukumar jin dadin alhazai ta jiha sun tsayar da ranar fara jigilar Maniyyata.

NAHCON Sabo 750x430

Hukumar kula da aikin hajji ta ƙasa NAHCON ta gudanar da taro da sakatarorin hukumar jin dadin alhazai ta jiha inda suka amince cewa jigilar maniyyatan zuwa kasa mai tsarki ya kamata a fara jigilar maniyyata zuwa kasa mai tsarki daga ranar 9 ga watan Mayun 2025 zuwa 24 ga watan Mayu.

A jawabinsa na bude taron, shugaban NAHCON, Farfesa Abdullah Saleh Usman, ya tunatar da mahalarta taron cewa ganawar na cikin shirye-shirye na karshe kafin a fara aikin Hajjin 2025.

Ya kuma yi kira ga Jihohin da su kara sabunta Hukumar NAHCON akan matakin da kowace jiha ta samu a fannin samar da Biza, allurar rigakafi, siyan jakunkuna da sauran su.

A yayin taron, kwamishinan NAHCON mai kula da ayyuka, Prince Anofiu Elegushi, ya bayyana cewa an baiwa kamfanin Air Peace alhazai 5,128 daga jihohin Abia, Akwa Ibom, Anambra, , Bayelsa, Benue, Borno, Cross River Delta, Ebonyi, Edo, Ekiti, Enugu, Imo, Kogi, Ondo, Rivers, Taraba State.

A daya bangaren kuma, kamfanin FlyNas, an ware masa maniyyata 12,506 daga babban birnin tarayya Abuja, Kebbi, Legas, Ogun, Osun, Sokoto da Zamfara.

Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar NAHCON, Fatima Usara ta sanya wa hannu, ta ce FlyNas ya kawo jiragen sama 9 domin gudanar da aikin.

Karin karatu: Sojoji sun kama wani mutum bisa zargin yin garkuwa da mutane a Kano, tare da kwato makamai

Kamfanin Max Air zai jigilar alhazai daga jihohin Bauchi, Gombe, Jigawa, Kano, Katsina, Kwara, Oyo da Plateau. Kamfanin jirgin ya yi alkawarin kammala jigilar maniyyata 15,203 nan da ranar 24 ga Mayu. Za a tura jirage biyu don gudanar da aikin – B747 mai karfin 400 sai na biyu mai karfin 560.

Kamfanin Umza an ware masa mahajjata 10,163 daga jihohin Kaduna, Adamawa, Nasarawa, Neja da Yobe. Umza yana tura jirage biyu – B747 mai karfin 477 da B777 mai karfin 310.

An yi lissafin rabon jigilar alhazai na shekarar 2025 akan jimillar mahajjata 43,000.

Kwamishinan tsare-tsare, bincike, kididdiga, yada Labarai Farfesa Abubakar Yagawal, ya sanar da taron matakin shirye-shiryen Hukumar ta fuskar kula da asibitocin da aka tabbatar an ware a Makkah da Madina, da raba katinan ganin likita ga jahohi, sannan daga karshe ya tunatar da su kada su sanya mata masu juna biyu aikin Hajji.

Jiragen za su rufe aikin daga 13 ga watan Yuni zuwa 2 ga Yuli.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here