Sojoji sun kama wani mutum bisa zargin yin garkuwa da mutane a Kano, tare da kwato makamai

IMG 20250422 WA0072 750x430

Dakarun rundunar tsaro ta hadin gwiwa ta Tundun Wada sun kama wani mutum mai shekaru 55 da ake zargi da yin garkuwa da mutane a wani samame da jami’an tsaro suka kai a kauyen Sumana da ke karamar hukumar Tundun Wada a jihar Kano.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta 3 Kaftin Babatunde Zubairu ya rabawa manema labarai a ranar Talata.

A cewar sanarwar, an kama wanda ake zargin ne a ranar 20 ga watan Afrilu.

Sanarwar ta ce an gurfanar da wanda ake zargin a gaban Kwamandan rundunar, Birgediya-Janar. Ahmed Tukur, wanda ya yi bikin Easter tare da sojojin Forward Operating Base (FOB) Falgore, a karamar hukumar Doguwa, Kano.

A cewar sanarwar, an gano tarin makamai, alburusai da sauran muhimman abubuwa yayin samamen.

An gano cewa, kayayyakin da aka kwato sun hada da bindiga kirar AK-47 guda daya, bindigar Den daya, harsashin bindiga mai girman 9mm, da kakin kamun kifi guda daya.

Haka kuma an samu nasarar kwato wata rigar kamun namun daji guda daya da kuma kujerar babur Bajaj, wadanda ake zargin ana amfani da su wajen boye makamai.

Sanarwar ta ce, Tukur ya yaba da kokarin da sojojin ke yi, yayin da ya jaddada aniyar rundunar sojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro, na hada kai da hukumomin yankin wajen dawo da zaman lafiya da tsaro, a cikin al’umma.

Sanarwar ta kara da cewa, a halin yanzu wanda ake zargin yana tsare kuma ana gudanar da bincike na farko. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here