Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, zai yi jawabi ga jama’ar jihar da misalin ƙarfe 6 na yammacin yau domin gode wa manyan masu ruwa da tsaki bisa mayar da zaman lafiya da kuma sake tabbatar wa al’umma da kudirin gwamnatinsa.
Fubara ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan dawowarsa Fatakwal a ranar Juma’a, inda dimbin jama’a suka tarbe shi a filin jirgin sama cikin murna.
Ya ce: “Zamu yi jawabi ga jama’a da ƙarfe 6 na yamma a hukumance, kuma a cikin wannan jawabi za mu nuna godiya ga kowa da kowa da ya ba da gudunmawa wajen dawo da zaman lafiya a wannan jiha.”
Dawowar gwamnan ta biyo bayan dage dokar ta-baci da Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya sanya a watan Maris 2025, wadda ta haifar da dakatar da Fubara, mataimakinsa da kuma Majalisar Dokokin Jihar Ribas saboda rikicin siyasa da na majalisa.
Wannan dokar ta-baci ta ɗauki tsawon watanni shida, inda aka soke ta a ranar 17 ga Satumba, kuma aka dawo da tafiyar da mulki ta dimokuraɗiyya a jihar.
Ana sa ran jawabin Fubara zai ƙara kwantar wa jama’a hankali tare da nuna sabuwar shirin gwamnatinsa bayan rikicin siyasar da aka shafe lokaci ana fama da shi.













































