Harin Amurka: Najeriya ce ta ba da bayanan sirri, aka amince da aikin – Gwamnatin Tarayya

Bola Tinubu Tinubu uk 750x430

Ministan harkokin waje Yusuf Tuggar ya bayyana cewa Nijeriya ce ta bayar da muhimman bayanan sirri da suka kai ga harin sama da Amurka ta kai kan wuraren ’yan ta’adda a cikin ƙasar, tare da amincewa da aikin a hukumance kafin a aiwatar da shi.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar talabijin ta Channels a ranar Juma’a, kwana guda bayan Amurka ta tabbatar da cewa ta gudanar da harin a matsayin wani ɓangare na ayyukan yaƙi da ta’addanci.

Ya jaddada cewa aikin ya samo asali ne daga ci gaba da haɗin gwiwar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka, ba tare da wata manufa ta addini ba.

Tuggar ya bayyana cewa an gudanar da tattaunawa mai zurfi tsakanin jami’an Nijeriya da manyan jami’an Amurka, inda aka cimma matsaya kafin a gabatar wa Shugaba Bola Tinubu bukatar amincewa da aikin.

Karanta: Shehu Sani ya yi martani kan hare-haren sojin Trump a Nijeriya

Ya ce an kuma yi daidaito kan yadda bayanan da za su fito bayan harin za su bayyana aikin a matsayin na yaƙi da ta’addanci tare da haɗin gwiwar ƙasashen biyu.

Ministan ya ce Nijeriya ta dade tana neman ƙarfafa haɗin gwiwa da Amurka da sauran ƙasashe domin magance matsalar ta’addanci, yana mai bayyana harin a matsayin tabbaci ga dabarun tsaron gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Ya ƙara da cewa manufar Nijeriya ita ce yin aiki tare da dukkan abokan hulɗa da ke da niyyar yaƙi da ta’addanci, ba tare da la’akari da addini ko ainihin waɗanda abin ya shafa ba, yana mai cewa duk wani nau’in ta’addanci abin ƙin yarda ne, ko da a wane suna ake aikata shi.

Gwamnatin tarayya ta tunatar da cewa Shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya tabbatar da kai harin sama kan wuraren da ake zargin ’yan ta’adda ke amfani da su a Nijeriya, yayin da jami’an Amurka suka bayyana cewa an gudanar da aikin ne bisa bayanan sirri da aka raba tare da haɗin kai da amincewar gwamnatin Nijeriya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here