Tsohon sanata Shehu Sani ya bayyana hare-haren sama da aka ruwaito cewa an kai kan wuraren ’yan ta’adda a arewa maso yammacin Nijeriya a matsayin mataki mai nauyi, tare da jaddada cewa dole Nijeriya ta ɗauki cikakken nauyin tsaronta da kanta a ƙarshe.
Shehu Sani ya bayyana matsayinsa ne ta shafin sada zumunta na X da aka tabbatar nasa, bayan shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya sanar da cewa sojojin Amurka sun kai hare-haren sama masu muni kan ’yan ta’addar Daular Musulunci a arewa maso yammacin Nijeriya.
Shugaban ƙasar Amurka ya nuna cewa an kai hare-haren ne bisa umarninsa kai tsaye, yana zargin ’yan ta’addar da kai munanan hare-hare da kisan fararen hula a yankin, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a cikin gida da wajen Nijeriya.
A wani rubutu daban, sakataren tsaron Amurka Pete Hegseth ya bayyana cewa Amurka ta yi aikin ne tare da haɗin gwiwa da goyon bayan gwamnatin Nijeriya, alamar cewa akwai fahimta da haɗin kai tsakanin ɓangarorin biyu a fannin tsaro.
Da yake mayar da martani, Shehu Sani ya nuna cewa idan da gaske an gudanar da hare-haren ne a matsayin aiki na haɗin gwiwa tsakanin hukumomin Nijeriya da rundunar sojin Amurka ta Afrika, to hakan babban mataki ne mai muhimmanci wajen fuskantar barazanar tsaro da ke addabar yankin.
Karanta: Gwamnatin tarayya ta tabbatar da hare-haren sama na Amurka kan wuraren ’yan ta’adda a Nijeriya
Ya bayyana ’yan ta’addar da ke aiki a wasu sassan ƙasar a matsayin barazana mai tsanani ga zaman lafiyar ƙasa, yana mai cewa su kamar cuta ce da ke lalata al’umma, tare da jaddada cewa ba su da bambanci wajen kai hari kan mabiya addinai.
Sai dai ya yi gargaɗi kan dogaro da ƙasashen waje wajen tabbatar da tsaro, yana mai cewa zaman lafiya na dindindin dole ne ya samo asali daga cikin gida, domin ko da taimako ya zo daga waje, ba zai maye gurbin cikakken alhakin da Nijeriya ke da shi na kare kanta ba.












































