Wata gobara ta tashi a babbar kasuwar Balogun a Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya.
Rahotonnin sun ce wutar ta kama a inda ake sayar da takalman mata a hawa na biyar.
Kawo yanzu dai ba a san musababbain tashin wutar ba.
Tun farko dai gobarar ta kama hawa na biyar kafin ta gangaro zuwa hawa na huɗu har zuwa na uku
Wani ganau ya shaida wa BBC cewa wutar ta tashi ne da misalin ƙarfe 9 na safe a lokacin da mutane ke shirin fito da kayyakinsu.
Jami’an kashe gobara na ƙoƙarin kashe wutar, inda tuni kuma aka yi ƙoƙarin killace wutar domin ka da ta haura zuwa wasu sassa.
Gobarar ita ce ta biyu a cikin ƙasa da wata guda a jihar, inda ko a mako uku da suka gabata wata gobarar ta tashi a kasuwar da ake sayar da kayan motoci a unguwar Apapa.













































