Kwankwaso ya bude makarantar koyar da ilimin shugabanci

FB IMG 16664591002515143
FB IMG 16664591002515143

Tsohon gwamnan Kano, kuma dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a babban zaɓen shekarar 2023, Injiniya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya jagoranci bude cibiya (makaranta) ta koyar da ilimin shugabanci, wacce ya sanar a birnin Kwankwasiyya dake yankin karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano.

Kwankwaso ya bude cibiyar a yau Asabar, duk cikin bukukuwan shagalin cikarsa shekaru 66 a Duniya, wanda aka saba gabatarwa duk shakara, tare da bude wasu muhimman abubuwa, inda a bana ya gina tare da bude masallacin juma’a a gefen gidansa dake unguwar Bompai Kano, da kuma wannan cibiya ta koyar da shugabanci mai suna “Amana Leadership Institute LTD/GTE”

Yayin bude cibiyar, Kwankwaso na tare da dan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Bishop Isaac Idahosa, da yan kwamitin kolin jam’iyyar NNPP karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Farfesa Rufai Alkali, da sauran mutane daban daban.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here