Indiya ta haramta ayyukan kungiyar tabbatar da ‘yancin Musulmai

d521d91a ff58 41cb 8eca 170a69ef6f52
d521d91a ff58 41cb 8eca 170a69ef6f52

Gwamnatin Indiya ta sanar da haramta ayyukan wata fitacciyar kungiya da ke fafutukar tabbatar da ‘yanci Musulmi da masu alaka da ita tsawon shekara biyar.

Jami’ai a India na zargin kungiyar ta PFI da alaka da kungiyoyin masu ikirarin jihadi.

An bayyana PFI a matsayin kungiyar da ayyukanta suka saba dokoki.

A ranar Talata, ‘yan sanda sun kai samame ofisoshin kungiyar a jihohin kasar 7 tare da kama mutane sama da 100.

Magoya bayan kungiyar sun ce wannan dai wata bita da kullin gwamnatin BJP ta Hindu ce.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here