Gwamnan Jihar Kano ya nada sakataren gwamnati na wucin gadi

Abba Kabir Yusuf Kano Governor 750x430
Abba Kabir Yusuf Kano Governor 750x430

Gwaman jihar Kano Engineer Abba Kabir Yusuf, ya umarci shugaban ma’aikatan gwamnati Abdullahi Musa da ya kula da ofishin sakataren gwamnatin Kano.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da skataren yada labaran Gwamnan Malam Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar aka rabawa manema labarai a Kano.

Nadin Abdullahi Musa na zuwa ne biyo bayan balaguron duba lafiya da sakataren gwamnatin jihar Dakta Abdullahi Baffa Bichi ya yi zuwa kasar Saudiya.

Karanta Kari:Gwamnatin kano ta fitar da Nera Milyan 300 ga daliban kano dake karatu a jami’ar Cyprus.

A cikin wata wasika da shugaban ma’aikatan fadar gwamantin Kano Shehu Wada Sagagi ya sanyawa hannun yace shugaban ma’aikatan gwamnatin Kanon zai ci gaba da lura da ofishin sakataren gwamnatin jihar har zuwa lokacin da zai dawo daga jinya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here