Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara wa’adin shekara guda ga mukaddashin kwanturolan Janar na hukumar shige da fice ta Kasa, Idris Isah Jere.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa an nada Idris Isah Jere a matsayin mukaddashin kwanturola Janar na Hukumar tun a watan Satumbar shekarar 2021 bayan ritayar Kwanturola Janar na lokacin, Muhammad Babandede.
Idris Isah Jere, a lokacin shi kuma ya kasance mataimakin Kwanturola Janar mai kula da harkokin kudi na hukumar.
A wata takarda mai taken: SAKE NADA SABON KWANTUROLA-JANAR NA HUKUMAR KULA DA SHIGE DA FICE TA KASA, mai kwanan watan 22 ga Afrilun, 2022, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ya sanar da tsawaita wa’adin Kwanturolan hukumar.
Wata wasikar da jaridar Solacebase ta gani kuma aka aikewa da Mai girma Ministan Harkokin Cikin Gida, ta ce karin wa’adin na mukaddashin Kwanturola Janar din ya fara aiki tun daga ranar 24 ga watan Afrilun 2022.
Hakan dai ya biyo bayan wasikar da aka aikewa ministan tun a ranar 15 ga watan Maris, din 2022.












































