Bikin Salla: hukumar FRSC za ta baza jami’ai 25,224 a faɗin Najeriya

FRSC New 660x381 1
FRSC New 660x381 1

Hukumar kiyaye afkuwar haɗurra ta Najeriya FRSC ta ce, ta tura jami’anta mutum dubu ashirin da biyar da ɗari biyu da ashirin da huɗu da za su yi aiki a faɗin Najeriya a yayin gudanar da bukukuwan Sallah.

Shugaban hukumar ta FRSC, Dakta Boboye Oyeyemi, ne ya bayyana hakan yau Talata a Abuja yayin wani taro da hukumar ta shirya dangane da bikin Sallar.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito cewa taken gangamin shi ne “Samun nasarar daƙile afkuwar haɗurra ta hanyar wayar da mutane kan su kula da bin ƙa’idojin hanya.”

Oyeyemi wanda ya samu wakilcin jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Bisi Kazeem, Ya ce an tura jami’an 25,224 da suka ƙunshi jami’ai 7,100 da hafsoshi 18,124, haka kuma an tura dakaru na musamman su 15,225 domin gudanar da ayyukansu a faɗin Najeriya.

Ya ce an yi hakan ne domin tabbatar da bin ka’idojin aiki da aka fitar a farkon atisayen.

Haka kuma Oyeyemi ya ce, an tura motocin sintiri 580, motocin ɗaukar marasa lafiya 92, manyan motoci 17 da babura 73 a wani bangare na aikin sintirin yayin Sallah.

Ya ce, rigunan aiki na musamman guda 2,096 da guda 1,000 na aikin zirga-zirga da ma’aunin gejin taya guda da na’urorin numfashi na zamani duk suna daga cikin kayayyakin da aka ware domin gudanar da ayyukan.

Ya ƙara da cewa, sansanonin kula da ababen hawa guda 10 da ma’aikata za su riƙa yin aiki ne ciki sa’o’i 24 har tsawon kwanaki 7 domin daƙile cunkoson ababen hawa a lokacin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here