Wani babban limamin coci, Felix Aluko, ya ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan zai koma fadar Aso Rock dake Abuja matukar ya yanke shawarar tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.
Aluko, babban limamin cocin Resurrected Assembly wato GROM shi ne ya bayyana hakan ranar Talata a Abuja.
Ya ce da ikon Allah Jonathan zai dawo a shekarar 2023 matsayin shugaban kasa idan har ya tsaya takara.
“Don haka ta faru, dole ne tsohon shugaban kasar ya fice daga tsarin siyasarsa na yanzu, (Jam’iyyar PDP), kuma ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar APC.
Limamin, ya yi gargadin cewa tsohon shugaban kasar ba zai sake zama shugaban Najeriya ba idan ya ki ya tsaya takara a zabe mai zuwa.
“Dole ne ya daidaita tunaninsa domin cika burinsa na samun damar karasa wa’adin zangonsa na biyu a matsayin shugaban kasa.
Kamfanin dillancin labarai NAN ya ruwaito cewa Jonathan ya ce bai gama yanke shawarar ko zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2023 ko ba zai tsaya ba.
Jonathan ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani ga magoya bayansa da suka yi zanga-zangar lumana a ofishinsa da ke Abuja ranar Juma’a, inda suka bukaci ya tsaya takarar shugabancin kasa a zaben shekaramai zuwa ta 2023.
Kazalika Jonathan, ya shaidawa magoya bayansa cewa “kawai ku zuba ido”.













































