Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da babbar daraktar hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA), Hajiya Zubaida Umar, sun kai ziyarar jaje ga wadanda suka jikkata sakamakon hare-haren bam da suka faru a ranar Litinin a Maiduguri.
Shettima, wanda ya yi magana da manema labarai jim kadan bayan ziyarar, ya mika sakon ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar jihar Borno da yankin Arewa maso Gabas, musamman iyalan wadanda suka rasa rayukansu a hare-haren kunar bakin wake guda uku da suka faru a ofishin gidan waya, kasuwar Monday da kuma babban kofar jami’ar Maiduguri da asibitin Koyarwa.
Mataimakin shugaban kasa da shugabar NEMA sun gana da wasu daga cikin wadanda suka jikkata a cibiyar kula da masu raunuka, inda suka yi addu’ar Allah ya jikansu da rahama ga wadanda suka mutu, tare da rokon samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.
Ya bayyana cewa sun je ne domin jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar Borno da yankin Arewa maso Gabas kan wannan mummunan lamari da ya afku.
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a dukkan sassan kasar.
Ya kara da cewa gwamnati ta hada kai da NEMA da kuma NEDC domin bayar da tallafi ga wadanda abin ya shafa, tare da godewa kafafen yada labarai kan goyon bayan da suke bayarwa.
Ya tabbatar da cewa NEMA za ta fara rabon kayan jinya da kayan tallafi ga wadanda abin ya shafa da iyalansu daga ranar Alhamis.













































