Kamfanin Fridabs SolaceBase Communication, masu wallafa jaridar SolaceBase, ya shirya taron buda baki na shekara-shekara ga ma’aikata, abokan hulda da baki a matsayin wani bangare na ayyukan kwanaki goma na karshe a watan Ramadan.
Taron da aka gudanar a ranar Talata ya hada ma’aikatan kamfanin tare da kwararru daga fannoni daban-daban, da kuma ‘yan uwa da abokai, cikin yanayi na tunani da zumunci.
Daga cikin wadanda suka halarta akwai Farfesa Umaru Pate, tsohon shugaban jami’ar tarayya ta Kashere, da kuma Barrista Ahmad Abubakar Gwadabe, shugaban Nigerian Bar Association reshen Ungoggo.
Haka kuma, manyan lauyoyi, likitoci da kwararrun kafafen yada labarai sun halarci taron.
Bakin da suka halarci taron sun yabawa SolaceBase kan jajircewarta wajen aikin jarida mai gaskiya da kuma rawar da take takawa wajen inganta aikin yada labarai mai inganci da nagarta.
Da yake jawabi a baya, mai wallafa kuma babban jami’in gudanarwa na SolaceBase, Abdullateef Abubakar Jos, ya nuna godiya ga bakin da suka amsa gayyatar kamfanin duk da cunkoson ayyukansu.
Ya ce an shirya buda bakin na shekara-shekara ne domin nuna godiya ga ma’aikata da kuma kara dankon zumunci tsakanin kamfanin da abokai da abokan hulda.
A cewarsa, taron yana kuma bayar da dama ga yin tunani da addu’o’i, musamman a cikin kwanaki masu muhimmanci na karshe na watan Ramadan.












































