Manoma a Kano sun tafka muguwar asara sakamakon ambaliyar Dam

IMG 20220912 WA0247 750x430 1
IMG 20220912 WA0247 750x430 1

Manoma a Kiru, Kura Bebeji da wani bangare daga Bunkure da kuma Kumbotso a cikin jihar Kano sun bayyana yacce suka tafka muguwar asara sakamakon ambaliyar dam din Tiga, inda ruwa ya mamaye gonakin su.

Binkicen da jaridar solacebase ta gudanar ya bayyana cewa ambaliyar dam din ta lalata amfanin ganaki da dama.

Malam Aminu Usman manomi ne a kauyen Kubaraci ya ce ruwa ya yi awan gaba da amfanin gonar sa baki daya.

Inda ya kara da cewa manoma da dama sun rasa amfanin gonakin su sakamakon ambaliyar dam din.

Shu’aibu Dorawa shima manomi ne da ambaliyar ta shafa, ya bayyanawa jaridar solacebase yacce ruwan yayi awan gaba da shinkafar da ya shuka a gonar sa mai fadin gaske.

Yace shekarar data gabata ruwan sama ya dauke da huri wanda hakan ya bashi matsala sosai, shi’isa bana yake da karfinn gwaiwar cewa zai sami riba mai yawa sakamakon ruwan saman da ya wadata a bana, sai kuma wannan iftila’i na ambaliyar ruwa ya afkawa gonar tasa.

Yayin da jaridar ta tun-tubi shugaban kungiyar manoman jihar Kano AFAN, Alhaji Abdulrasheed Magaji Rimin Gado, yace sunanan suna karbar bayanan manoman da ambaliyar dam din ta shafa.

“Gaskiya ne dam ya yiwa manoma da dama barna, abin rashin jin dadi ne ace lokacin da manoma suke da burin samun amfanin gona mai yawa wannan abu kuma ya faru, mun bada umarni ga shugananin mu na kanan hukumomi da su karbe bayanan duk manoman da abin ya shafa.” Inji shi.

A juma’ar data gabata ne dai wani rahoto yake nuni da cewa dam din Tiga ya balle inda yayi manona da dama barna.

Sai dai kuma hukumar dake kula da dam din Hadejia Jama’are HJRBDA, ta karyata rahotan inda tace dam din yanan cikin koshin lafiya.

Yayin da ya kai ziyara babban Darakta na hukumar ta HJRBDA, Ma’amun Da’u Aliyu ya ce dam din yana yanayi mai kayu wanda bai taba zama a irrin sa ba.

ya kara da cewa ruwan ba wai ballewa yayi ba, an sake shine domin rage shi.

A wani bangaran kuma wakilan gwamnatin tarayya wanda dan majalisar tarayya mai wakiltar Rano/Bunkure/Kibiya,  Alhaji Kabiru Alhassan Rurum , ya jagoran ta sun kai ziyara wajan domin ganin barnar da ambaliyar tayi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here