Gwamnatin tarayya ta dauki ‘yan sanda 40,000 aiki a cikin shekaru 4 – Buhari

071336B1 5EC3 4FF4 A4BE BDE91F0DA516
071336B1 5EC3 4FF4 A4BE BDE91F0DA516

Gwamnatin tarayya ta ce ta dauki ‘yan sanda 40,000 aiki a cikin shekaru hudu da suka gabata, a kokarinta na sake karfafawa da inganta jami’an rundunar domin tunkarar kalubalen tsaro da ake fuskanta a kasar nan.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne a cikin jawabinsa, yayin bude taron kwana biyu ga manyan jami’an ‘yan sanda a Uyo, ranar Talata.

Buhari wanda ya samu wakilcin ministan harkokin ‘yan sanda, Dokta Maigari Dingyadi, ya ce gwamnatin tarayya ta kuma amince da dokar asusun kula da ‘yan sandan Najeriya tare da gudanar da nazari kan albashi da alawus-alawus na manya da kananan ‘yan sanda, a wani mataki na tabbatar da tsaro da kara kwarjini ga Rundunar.

Ya ce sauran kokarin da ake yi na inganta ayyukan rundunar sun hada da; kafa kwamitin tantance bukatu na ‘yan sandan Najeriya karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.

Ya kara da cewa, gwamnatin tarayya ta kuma sanya hannu kan dokar tsarin ‘yan sandan Najeriya na shekarar 2020 a matsayin wani bangare na matakan sake fasalin rundunar ‘yan sandan.

“Wannan gwamnatin ta ba da fifiko ga sake fasali da samar da kayan aiki tare da gyara wanda ake da su, tare da samar da  muhimman gine-ginen da zasu tallafawa rundunar gudanar da ayyuka.

“Hakika, tun da aka fara tafiyar dimokuradiyya a 1999, babu wata gwamnati da ta nuna himma wajen kyautatawa da jin dadin ‘yan sandan Nijeriya da ci gaban hukumomin ‘yan sandan Nijeriya kamar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari mai ci a yanzu.

“Wannan ya tabbata ne a kan amincewar da shugaban kasa ya bayar ga kudirin asusun tallafawa ‘yan sandan Najeriya da kuma gaggawar kaddamar da kwamitin amintattu.

“Bugu da kari, gwamnatin tarayya ta kuma amince da daukar jami’an ‘yan sanda 40,000 a tsawon shekaru hudu, a matsayin hanyar da za a bi wajen magance babban gibin da ake fama da shi na aikin ‘yan sandan kasa,” in ji Buhari.

Shugaban ya kuma yabawa Majalisar Dokoki ta Kasa da Kungiyar Gwamnonin Najeriya, bisa goyon bayan da suke baiwa rundunar ‘yan sanda.

Ya ba da tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da ba da fifiko ga kokarin da ake yi na sake farfado da aikin injiniya da kuma samar da kayan aiki ga rundunar domin tunkarar kalubalen tsaro da ke kara rikidewa a kasar nan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here