Gwamnatin tarayyar ta dakatar da shirin ƙarin harajin kiran waya sadarwa.
Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki a Fasahar Zamani, Isa Pantami ne ya sanar da dakatarwar a yau Litinin yayin taron kaddamar da kwamitin shugaban kasa haraji kan hanyoyin sadarwa don bunƙasa ɓangaren tattalin arziki ta hanyar fasahar zamani a Abuja.
Ministan ya ce tun tuni fannin sadarwa ya cika da harajai da yawa.
Gwamnatin tarayya ta hannun ofishin kasafin kudi na tarayya a baya ta bayyana cewa za ta fara aiwatar da shirin fitar da kudaden da ta ke bukata a kan harkokin sadarwa da abubuwan sha a shekarar 2023.
Sai dai Pantami ya ci gaba da cewa ba ya goyon bayan aiwatar da wannan harajin da zai kara tsadar harkokin sadarwa ga ‘yan Najeriya.












































