Majalisar gudanarwa ta Jami’ar tarayya ta Kashere a Jihar Gombe ta amince da nadin babban magatakarda da Bursar daga ranar 11 ga Fabrairun 2025.
SolaceBase ta ruwaito cewa Majalisar ta dauki matakin ne a taronta na yau da kullun karo na 25.
Wata sanarwa da mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Umaru A. Pate ya fitar tare da sanya hannun a ranar Talata ta ce wadanda aka nada sun hada da Alhaji Nasir Lawan Abdullahi a matsayin magatakarda yayin da Isa Adamu Amaza a matsayin Bursar.
Sanarwar ta ce, har zuwa lokacin da aka nada shi magatakardar Jami’ar tarayya ta Kashere (FUK), Nasir Lawal Abdullahi shi ne magatakardar Kwalejin Ilimi ta tarayya da ke Jama’are a Jihar Bauchi.
Karin labari: Shugaban jami’ar KHAIRUN ya samu karramawa daga NIM a matsayin jajirtaccen shugaba
Ya fara aiki a matsayin jami’in gudanarwa a jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) Bauchi inda ya kai matsayin babban mataimakin magatakarda a shekarar 2018.
Sabon Bursar (FUK) Isa Adamu Amaza ya kasance, har zuwa lokacin da aka nada shi a FUK, Ag. Daraktan Kwalejoji da tsangayar ilimin akanta na Digiri na biyu a Sashen Bursary na Jami’ar Maiduguri inda ya fara aikinsa a matsayin Akanta har ya kai matsayin mataimakin Bursar a 2019.
A yayin da suke taya su murnar zaɓen da kuma tattaunawa da su, shugaban majalisar, Farfesa Williams Olushola Aderounmu da shugaban jami’ar Farfesa Umaru A. Pate sun ce nadin na su ya dogara ne da kwazo da gogewa.