Dangote ya sanya wa titin matatarsa sunan Shugaba Tinubu

A file photo of Dangote Refinery (1)

Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, ya sanya wa babban titin da ke kan hanyar zuwa matatar man sa da ke birnin Lagos sunan shugaban kasa Bola Tinubu, domin karrama gudunmawar da ya bayar wajen aikin.

Dangote ya sanar da hakan ne yau Alhamis yayin da yake kaddamar da titin wanda ke hanyar tashar ruwa ta Deep Sea a Lagos wanda ya hada kamfanin taki na Dangote da mahadar titin zuwa Eleko.

“Ya mai girma shugaban kasa, bari in fadi abu daya kawai, babbar hanyar da za ta shiga matatar man yanzu za a kira ta da Titin Bola Ahmed Tinubu.” in ji Dangote

Haka kuma, attajiri, ya yaba da jagorancin Tinubu, inda ya kwatanta shi a matsayin mai karfin zuciya, kuma mai burin samar da ci gaba kana wanda gwamnatinsa ta sake sabunta kwarin gwiwa kan saka hannun jari a kamfanoni masu zaman kansu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here