Gidauniyar Tony Elumelu (TEF) ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar dala miliyan 6 da ofishin kula da harkokin raya kasa na Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) domin tallafa wa ‘yan kasuwan Afirka.
A cikin wata sanarwa da Moyo Awotile, shugaban sashen kasuwanci da sadarwa na TEF ya fitar ranar Laraba, ya ce kawancen da aka sanya wa hannu a taron gwamnatocin duniya, ya kuma shafi gidauniyar Khalifa Bin Zayed Al Nahyan, mai alaka da Erth Zayed.
Sanarwar ta kara da cewa, “Yarjejeniyar da aka sanya wa hannu, a taron gwamnatocin duniya, wanda ya kafa TEF, Tony O. Elumelu, da Darakta Janar na Gidauniyar Khalifa Bin Zayed Al Nahyan, Mohamed Haji Al Khoori, ya nuna cewa dukkanin kungiyoyin biyu sun sadaukar da kansu wajen bunkasa tattalin arziki da kasuwanci a fadin Afirka.”
Karanta: Gwamnatin Kano na shirin daidaita kasuwanni don inganta kudaden shiga
“Ta hanyar wannan haɗin gwiwa, Gidauniyar Khalifa Bin Zayed Al Nahyan za ta ba da gudummawar ƙwarewar gidauniyar Tony Elumelu da ikon aiwatar da ayyukan kasuwanci ta hanyar Shirin Kasuwancin Tony Elumelu, wanda ya jagoranci horar da harkokin kasuwancida kuma ba da kuɗaɗen jari ga ‘yan kasuwa na Afirka.
Da yake magana game da yarjejeniyar, Tony Elumelu, wanda ya kafa TEF, ya ce karfafawa ‘yan kasuwa ba kawai wani abu ne na ɗabi’a ba, yunkuri ne na dabarun saka hannun jari a makomar Afirka.
A cewar sanarwar, haɗin gwiwa da gidauniyar Khalifa Bin Zayed Al Nahyan ita ce ta farko da wata ƙungiyar agaji ta yankin Gulf.
Zuwa yanzu dai an sanya wa’adin ranar 1 ga watan Maris, don gidauniyar ta ci gaba da karɓar neman izini daga matasa kananan ‘yan kasuwa a duk faɗin Afirka tare dauki da sabbin dabarun kasuwancin da ba su wuce shekaru biyar akan TEFConnect.