Gwamnatin Kano na shirin daidaita kasuwanni don inganta kudaden shiga

WhatsApp Image 2025 02 02 at 20.46.23

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana shirinta na daidaita kasuwannin ta domin inganta harkar hada-hadar kudi, da bin diddigin yadda ake tafiyar da harkokin tattalin arziki, da inganta samar da kudaden shiga.

SolaceBase ta ruwaito cewa shirin ya kasance wani muhimmin batu da tattaunawa tsakanin kwamishinan kasuwanci, zuba jari da masana’antu, Alhaji Shehu Wada Sagagi, da kwamitin majalisar masarautu kan harkokin tattalin arziki da zamantakewa a ranar Lahadi.

Sagagi ya jadadda cewa, daidaita kasuwannin zai baiwa gwamnati damar sanya ido kan harkokin kudi tare da kara fahimtar yadda kudaden ke tafiya aKano.

Ya ci gaba da cewa, “Mun tattauna kan yadda za a rika sanya hannayen jari a kasuwanninmu ta yadda gwamnati za ta iya bin diddigin yadda ake gudanar da harkokin tattalin arziki da sanin hakikanin adadin kudaden da ke kai kawo.

Taron ya kuma yi nazari kan dabarun farfado da masana’antu da kuma farfaɗo da martabar Kano a fannonin da suka hada da noman tufafi, masaku, da kere-kere, har ma ya jaddada muhimmancin tabbatar da samar da wutar lantarki mai inganci ga masana’antun tufafi da aka kafa kwanan nan a fadin kananan hukumomi 44 na jihar.

Shugaban kwamitin Masarautar Kano Alhaji Shehu Muhammad wanda kuma shi ne Sarkin Shanun Kano, ya bayyana irin rawar da kwamitin ke takawa wajen baiwa gwamnati shawara kan harkokin tattalin arziki.

Yana mai cewa, tattalin arzikin Kano a tarihi ya kasance kasuwanci ne da masana’antu ke tafiyar da shi, wanda hakan ya sa ya zama dole a zamanantar da ayyuka da kuma rage dogaro ga kasuwannin waje.

“Mutanen mu na kashe biliyoyin kudi domin yin balaguron zuwa Aba da Onitsha a duk wata don sayan kaya a masaku duk da cewa suna da albarkatun da suke da shi a nan Kano.

Tattaunawar ta kuma tabo batun sake farfado da kwamitin tattalin arziki da saka hannun jari na jihar Kano wanda ya shafe shekaru a kwance

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here