Shugaban kungiyar ci gaban al’ummar Oke-Oyi na karamar hukumar Ilorin ta Gabas a jihar Kwara, Alhaji Ahmed Seriki, ya yi kira ga IBEDC da ta maido da wutar lantarki kamar yadda aka saba, bayan shafe watanni 18 na dauke wuta a yankin.
A wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Lahadi a Ilorin, Seriki ya yi tir da lamarin tare da yin kira ga Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Ibadan da ya gaggauta magance matsalar.
Lamarin dai, in ji shi, yana shafar harkokin kasuwanci a yankin, da kuma tabarbarewar tattalin arziki.









































