COVID-19: Majalisar wakilai ta umarci ma’aikatan kashe gobara su dawo da Naira Biliyan 1.48

Majalisar, wakilan, Najeriya, kwato, jirage, NCAT, Zariya, sayar
Majalisar wakilan Najeriya ta sha alwashin kwato jirage 2 na Bell 206L4 BZB da Bell M2061- L4 na kwalejin fasahar jiragen sama ta Najeriya NCAT Zariya da aka...

Kwamitin Kididdigar Jama’a na Majalisar Wakilai ya umarci Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya da ta mayar da kudaden da suka kai Naira biliyan 1.48 cikin mako guda zuwa asusun tarayya, kasancewar kudaden shiga tsakani da ta samu na annobar COVID-19 amma ba za ta iya tantance su ba.

Kwamitin da Bamidele Salam ya jagoranta ya bayar da wannan umarni ne a ranar Larabar da ta gabata biyo bayan gazawar da hukumar ta yi a zaman binciken a karo na uku.

Karanta wannan: Ma’aikatan BDC sun bayyana dalilin daina ayyukansu a Abuja

Mataimakin shugaban kwamitin Jeremiah Umar ne ya gabatar da bukatar a mayar da kudaden inda ya ce “sauran hukumomi da dama sun bayyana a gaban wannan kwamiti, kuma ana ci gaba da bincike. Ban ga dalilin da zai sa hukumar kashe gobara za ta yi watsi da wani kwamiti irin wannan ba.”

Umar ya kara da cewa tun da hukumar ba za ta iya bayyana a gaban ’yan majalisar ba don kawar da cece-kucen da ke tattare da kashe-kashen da aka yi na COVID-19, abin da ya dace shi ne a mayar da kudaden da suka kai Naira Biliyan 1.48 da ta tara a shekarar 2020.

Karanta wannan: Har yanzu zafin shan kaye ne ke damun Atiku – Tinubu

Wannan ya zo ne a daidai lokacin da kwamitin ya yi sabbin gayyata ga wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya da su bayyana su amsa tambayoyi daban-daban da ke gaban su daga ofishin babban mai binciken kudi na tarayya kan biliyoyin Naira da aka ware a matsayin kudaden shiga tsakani na COVID-19.

Wadanda aka gayyata sun hada da ma’aikatar noma da samar da abinci ta tarayya, wadda ta samu Naira Biliyan 50.5 sai Ofishin akanta janar na Tarayya Naira Biliyan 33 da Ma’aikatar Harkokin Mata ta Tarayya da sauran hukumomi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here