Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da kashe Naira Biliyan 38.7 domin aiwatar da manyan ayyukan raya kasa da kuma biyan muhimman wajibai a fannoni daban-daban na jihar.
Gwamnan ya mince da hakan a taron majalisar zartarwa karo na 35 ta shafi tsaro, ilimi, gine-ginen hanyoyi, samar da ruwa, ayyukan kiwon lafiya, noma, makamashi da kuma biyan diyya ga al’ummomi da abin ya shafa.
Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Dawakin Tofa, ya fitar ta bayyana cewa majalisar ta kuma amince da kashe Naira Biliyan 3.77 domin muhimman ayyuka a fannin ilimi a fadin jihar.
Majalisar ta ware Naira Biliyan 1.69 domin biyan bashin masu samar da kayayyakin makarantu na kwana don shekarar karatu ta 2025 zuwa 2026, da Naira Miliyan 375 don sayen jakunkunan makaranta 50,000 ga dalibai, da kuma Naira Miliyan 369.9 don gyaran makarantar sakandare ta gwamnati da ke Mariri.
Haka kuma, an amince da kashe Naira Biliyan 1.32 domin sauya matsuguni tare da sake gina makarantar firamare ta Maikwatashi da ta Danwaire, tare da umarnin kammala ayyukan gina ajujuwa a kananan hukumomi 44 cikin wata guda domin dawo da inganci, tsaro da mutunci a makarantun gwamnati.
A bangaren tsaro da kiwon lafiya, majalisar ta amince da sayen babura 300 domin rundunar sintirin unguwanni, da kuma kashe Naira Biliyan 6.81 don gyaran cibiyoyin kiwon lafiya, tare da biyan diyya ga masu kadarori 5,015 na yankin Rimin Zakara.
Majalisar ta kuma amince da kashe Naira Biliyan 26.1 domin gina hanyoyi, ayyukan samar da ruwa da biyan diyya, ciki har da Naira Biliyan 16.29 don aikin hanyar Gwarzo–Tsaure–Tsanyawa.
Za’a kashe Naira Biliyan 2.22 don gyaran titin Murtala Mohammed Way, Naira Miliyan 398.2 don mataki na biyu na ayyukan samar da ruwa na Abba Kabir Yusuf, Naira Miliyan 182.1 don faɗaɗa bututun ruwan Hotoro, da kuma Naira Miliyan 111.7 don gyaran madatsar ruwan Gani, domin inganta zirga-zirga, samun tsaftataccen ruwa da bunƙasar tattalin arziki a jihar Kano.












































