Tinubu ya sauya sunan jami’ar tarayya ta Azare zuwa jami’ar Sheikh Dahiru Usman Bauchi

IMG 20251220 WA0010 2 750x430

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya sauya sunan jami’ar kimiyyar lafiya ta tarayya da ke Azare zuwa jami’ar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, domin girmama marigayi fitaccen malamin addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Shugaban ƙasar ya sanar da hakan ne a lokacin ziyarar ta’aziyya da ya kai wa gwamnatin jihar Bauchi da iyalan marigayin malamin ranar Asabar .

Ya ce, an yanke shawarar sauya sunan jami’ar ne domin adana tarihin gudummawar da Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bayar ga al’umma da addini.

Ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai kaunar bil’adama, wanda ya isar da ilimi mai amfani ga jama’a, tare da jajircewa wajen bautar Allah Madaukakin Sarki da hidima ga al’umma.

Shugaban ƙasar ya jaddada cewa sauya sunan jami’ar daga jami’ar kimiyyar lafiya ta tarayya ta Azare zuwa jami’ar Sheikh Dahiru Usman Bauchi wata hanya ce ta girmamawa da ɗaukaka tarihin rayuwar marigayin da tasirin da ya bari a ƙasa baki ɗaya.

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yaba wa shugaban ƙasar bisa ziyarar ta’aziyyar da ya kai wa gwamnatin jihar da iyalan marigayin, yana mai cewa zuwan shugaban ƙasar da kansa, bayan tura mataimakinsa Kashim Shettima a lokacin jana’izar, ya nuna irin girmamawa da kusanci da yake da shi da marigayin, iyalansa da al’ummar jihar.

A madadin iyalan marigayin, Dakta Bashir Sheikh Dahiru Bauchi ya bayyana godiya ga shugaban ƙasar bisa tura tawaga mai ƙima a lokacin sallar jana’iza da kuma ziyarar ta’aziyya da ya kai wa iyalan, yana mai bayyana hakan a matsayin alamar girmamawa da daraja ga Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa shugaban ƙasar ya tashi daga filin jirgin sama na Sir Abubakar Tafawa Balewa nan take bayan kammala ziyarar domin komawa birnin Legas.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here