Yan Ta Adda Sun kai Hari Jimi’ar Kogi

Gunmen 2

Halima Lukman

Ana fargabar sace dalibai da dama yayin da wasu ‘yan ta’adda suka kai hari a daren Alhamis a jami’ar Confluence University of Science and Technology, Osara, Okene a jihar Kogi.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun dira jami’ar ne da misalin karfe 9 na dare a daidai lokacin da daliban ke karatun jarabawar da za su yi.

Sun kama daliban a cikin zaurukan, suka fara dauke su; makarantar ta shiga cikin rudani, yayin da daliban da suka firgita a wasu zauruka suka yi ta tururuwa ta bangarori daban-daban.

A lokacin da jami’an tsaro na cikin gida da jami’an tsaro na yau da kullun da ke bakin kofar suka shiga tsakani da barayin, tuni suka yi nasarar sace wasu dalibai.

Amma kokarin ya rage barnar da aka yi saboda maharan ba su wuce dakunan farko guda uku ba,” inji majiyar jaridar Punch.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here