Dan Majalisar Wakilan Jigawa Dogon Yaro Ya Rasu

Dogonyaro

Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Babura/Garki ta jihar Jigawa a majalisar wakilai ta 10 Hon. Isa Dogonyaro, ya rasu.

A wata sanarwa da kakakin majalisar kuma shugaban kwamitin majalisar kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, Rep Akin Rotimi, Jr. ya sanyawa hannu a ranar Juma’a, majalisar ta ce ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya.

“Hon. Isa Dogonyaro ya kasance dan majalisa mai kwazo kuma mai kishin kasa wanda ya yi wa al’ummar mazabarsa da kasa hidima da kwazo. Ya kasance ginshiki a majalisar, inda ya bayar da gudunmawa sosai wajen samar da dokoki, musamman a fannin yaki da cutar kanjamau, tarin fuka, da yaki da zazzabin cizon sauro, inda ya zama mataimakin shugaban kwamitin majalisar.

“An zabe shi a jam’iyyar All Progressives Congress, Hon. Dogonyaro ya shahara da rikon amana da jajircewa da sadaukar da kai ga rayuwar al’ummar Najeriya. Za a yi kewar kasancewar sa a cikin zauren majalisar wakilai mai tsarki.
“Hon. Isa Dogonyaro ya kasance dan kishin kasa wanda ya kasance mai yawan fara’a kamar yadda shi haziki ne. Ya kulla zumunci mai karfi da Honourable Members daga dukkan sassan kasar nan. Ya bar matansa da ‘ya’yansa.

“A wannan lokaci na bakin ciki, tunaninmu da addu’o’inmu suna tare da iyalansa, mazabarsa, abokan aikinsa, da al’ummar Jihar Jigawa. Muna addu’ar samun karfi da ta’aziyya ga duk wadanda suka yi alhinin rasuwarsa,” in ji sanarwar.

Za a sanar da cikakkun bayanai game da shirye-shiryen jana’izarsa nan gaba kadan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here