Gwamnatin Tarayya ta bada hutun Babbar Sallah

Minister of Interior Dr. Olubunmi Tunji Ojo (1)

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Laraba 27 da Alhamis 28 ga watan Mayun shekarar 2026, a matsayin ranakun hutu don murnar bikin Babbar Sallah.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da babbar sakatariya a ma’aikatar, Magdalene Ajani, ta fitar ranar Litinin.

A cewar sanarwar, Gwamnatin Tarayya ta ayyana hakan don nuna girmamawar ga imani da al’adun miliyoyin Musulmi a fadin Najeriya da ke gudanar da bikin tare da al’ummar Musulmai a duniya.

Tunji-Ojo ya taya Musulman Najeriya da na wajen kasar murnar bikin, inda ya bayyana Sallar a matsayin biki mai ma’ana ga rayuwar wanda ya dogara kan sadaukarwa, biyayya ga Allah, da tausayi ga dan’adam.

Ministan ya bukaci ‘yan Najeriya su yi amfani da lokacin hutu wajen yin addu’a da yin tunani kan zaman lafiya, tsaro, da ci gaban kasar.

“Gwamnatin Tarayya na bukatar dukkan ‘yan Najeriya su yi amfani da wannan lokaci wajen addu’a da yin tunani cikin nutsuwa, tare da neman shiriyar Allah ga kasar yayin da take ci gaba da neman zaman lafiya, tsaro, da ci gaba ga kowane dan ƙasa,” in ji sanarwar.

Ya kuma yi kira ga ‘yan kasa da su Gina ruhin dan’uwantaka, hadin kai, da zama lafiya a lokacin bikin.

Gwamnatin Tarayya ta yi wa Musulmai a fadin kasar fatan yin bikin Babbar Sallah cikin lumana, albarka, da farin ciki.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here