Falasɗinawa sun fara azumin Ramadan yayin da ake ci gaba da gwabza faɗa a yankin tsakanin dakarun Isra’ila da sojojin Hamas kuma babu wata alamar cewa za’a cimma tsagaita wuta.
Isra’ila ta lalata muhallan akasarin al’ummar Gaza, yayin da a alokaci guda hukumomin bayar da agaji ke gargaɗin cewa mutane za su mutu saboda yunwa.
A daren da ya gabata an yi artabu bayan da ‘ƴan sandan Isra’ila suka hana ɗaruruwan matasa Falasɗinawa shiga masallacin Al Aqsa.
Karin labari: Abdulsalami ya nemi Nijar da Mali da Burkina Faso su koma ECOWAS
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu dai ya sha alwashin ci gaba da ruwan wuta a birnin Rafah da ke kudancin Gaza duk da gargaɗin da shugaban Amurka Joe Biden ya yi kan batun.
A cikin saƙonsa na Ramadan ga al’ummar Gaza, Biden ya ce Musulmai da dama a duniya za su yi azumi ne da Falasɗinawa a ransu.