Abdulsalami ya nemi Nijar da Mali da Burkina Faso su koma ECOWAS

Abdulsalami, Abubakar, Nijar, Mali, Burkina Faso, ECOWAS
Tsohon shugaban kasar Najeriya, kuma ɗaya daga cikin masu shiga tsakani kan rikicin ƙungiyar ECOWAS da jumhuriyar Nijar, Janar Abdulsalami Abubakar mai...

Tsohon shugaban kasar Najeriya, kuma ɗaya daga cikin masu shiga tsakani kan rikicin ƙungiyar ECOWAS da jumhuriyar Nijar, Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, ya yi kira ga ƙasashen yanki uku da su koma cikin ƙungiyar.

Wannan ne karon farko da mai shiga tsakanin ya furta cewa, ficewar Ƙasashen Burkina-Faso da Mali da kuma jumhuriya Nijar daga ECOWAS mayar da hannun agogo baya ne.

Karin labari: Anga watan Ramadana a Najeriya – Sarkin Musulmi

A cewarsa matakin ƙasashen zai iya kawo naƙasu ga tattalin arzikin yankin.

Janar Abdulsalami Abubakar ya yi kira ga ƙasashen uku da su dawo cikin garke a yi tafiya da su, domin sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here