Anga watan Ramadana a Najeriya – Sarkin Musulmi

Muhammadu Saad Abubakar III Sarkin Musulmi
Muhammadu Saad Abubakar III Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi ya sanar da cewa, a ranar Litinin 11 ga watan Maris ne za a fara azumtar Ramadana a Najeriya.

ya bayyana hakan ne a wani sakon kai tsaye da aka wallafa a shafin hukumar ganin wata ta kasa da misalin karfe 8:40 na dare a ranar Lahadi 10 ga watan Maris.

Wannan na nufin, ranar Litinin ce za ta zama ranar 1 ga watan Ramadana na hijirar Annabi SAW 1445, kamar yadda ya shaida.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here