Gwamnatin Kogi ta musanta shirin korar malamai saboda rashin goyon bayan APC

Yahaya Bello
Yahaya Bello
Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na Kogi, Wemi Jones, ya ce gwamnatin jihar ba ta da wani shiri na korar wani malamai.
Kwamishinan ya yi wannan karin haske ne a wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a a Lokoja, yayin da ya ke mayar da martani kan rahotannin da ke yawo a wasu sassan kafafen yada labarai na cewa “Gwamna Yahaya Bello ya bayar da umarnin korar malaman Kogi wadanda ba sa goyon bayan APC.”
Kwamishinan ya bayyana rahoton da ake yadawa a matsayin “labarai na karya, cikakken sharri, kazafi, kuma maras tushe”.
“Wannan hasashe ne na wasu marasa kishin kasa da ke yin kamfen din adawa da nufin haifar da rashin jituwa a tsakanin malamai da ma’aikata a jihar.
“A gaskiya ma, gwamnatin jihar na shirin fitar da jerin sunayen mutane 1,500 da suka yi nasara a ka ɗauke su aiki a matsayin malamai a makarantun sakandire na jihar a matakin farko na shirin daukar malamai.
“Don haka, rahoton da ake yaɗawa ƙarya ce ziryan,” in ji shi

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here