Wani shaidar Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Laifukan Kuɗi EFCC, David Jaiyeoba, ya shaida wa babbar kotun Babban Birnin Tarayya Abuja cewa an gano kuɗi har Dalar Amurka Miliyan 2.045 da kuma wasu takardun kadarori da ake alaƙanta su da tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele.
Jaiyeoba, wanda shi ne shaida na goma sha biyu na masu gabatar da ƙara kuma jami’in EFCC, ya danganta kuɗaɗen da kadarorin da wasu amincewar mu’amalolin banki da bayanan asusu da hukumar ta samu yayin bincikenta kan lamarin.
A yayin gabatar da shaidar da Daraktan Gurfanar da Masu Laifi na EFCC, Rotimi Oyedepo, ya jagoranta, shaidar ta bayyana takardun ciki na Babban Bankin Najeriya da suka nuna amincewa da biyan kuɗaɗe domin gyare-gyare, shimfiɗa lambuna, samar da wutar lantarki da kuma kayan daki a gidan aiki na tsohon gwamnan bankin da ke Ikoyi a Jihar Lagos.
Kotun ta samu bayanin cewa an gabatar da wasu takardu a matsayin hujjoji, ciki har da wata takardar cikin gida ta Babban Bankin Najeriya da ta amince da biyan kuɗi ga kamfanin Architeco Nigeria Limited domin ayyukan gyaran gidan Emefiele, tare da wata yarjejeniya da ta bayyana ayyukan shimfiɗa lambuna da kamfanin ya gudanar a kadarar Ikoyi.
Haka kuma, shaidar ta nuna wata takardar gida da ke neman amincewa da biyan Naira 97,998,416.38 ga Architeco Nigeria Limited domin samar da kayan ofis, inda aka nuna cewa Emefiele ne ya amince da wannan buƙata, tare da wata takarda da ta shafi sanya layukan wutar lantarki na musamman a gidan Ikoyi da ke ɗauke da shaidar biyan kuɗi da amincewar wanda ake tuhuma.
Shaidar ta kuma bayyana cewa EFCC ta rubuta wasiƙa zuwa Bankin Zenith domin bibiyar asusun bankin Emefiele, inda aka gabatar da martanin bankin a matsayin hujjoji, ciki har da wata mu’amalar cire kuɗi ta ranar 13 ga Janairu 2015 daga asusu mai lamba 2020000064, wadda ta nuna biyan naira miliyan huɗu ga Architeco Nigeria Limited.
Binciken ya kai ga kwato Dalar Amurka Miliyan 2.045 da wasu kadarori da takardun mallaka daga hedkwatar Bankin Zenith a Jihar Lagos, inda aka same su a hannun Collins Omeke, lauyan Emefiele, wanda ya bayyana cewa yana sayen kadarori da sarrafa takardun mallakarsu ne bisa umarnin wanda ake tuhuma, tare da karɓar kuɗaɗen waje musamman Dalar Amurka don wannan aiki, kuma wani ɓangare na kuɗin an yi amfani da shi wajen gyaran wasu kadarorin Emefiele.
A ƙarshen zaman kotun, masu gabatar da ƙara sun nemi ɗage shari’ar domin ci gaba da sauraro, inda lauyan kariya Matthew Burkaaa ya nuna damuwa kan maimaita hujjoji, yayin da alkalin shari’a Hamza Muazu ya bayyana cewa duk da yadda masu gabatar da ƙara ke nuna taka-tsantsan.
Kotun za ta ba su dama su gabatar da shari’arsu, tare da ɗage sauraron zuwa ranakun da aka tanada domin ci gaba da shari’ar.













































