An sako basaraken da aka yi garkuwa da shi a Ondo

Nigeria Kidnappings Bandits deputy
Nigeria Kidnappings Bandits deputy

Bayanan da aka samu daga ƴan’uwa sun ce an sako Oba Clement Omoola Jimoh ne jiya Laraba, inda aka kai shi asibiti domin duba lafiyarsa.

A makon da ya gabata ne aka sace basaraken, inda ya kwashe mako guda a hannun masu garkuwa da mutane.

Lamarin ya faru ne a lokacin da ƴan bindigan suka kutsa fadarsa da ke ƙaramar hukuma Akoko ta Yamma a ranar Alhamis ɗin makon jiya, inda suka ɗauke shi zuwa wani wuri na daban.

Daga baya ƴan bindigan sun buƙaci a biya maƙudan kuɗaɗe domin sako shi, sai dai an sulhunta a kan ƙasa da abin da suka buƙata, amma duk da haka ba a fayyace ko sai da aka biya kuɗin fansar kafin sako basaraken ba.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Najeriya a jihar ta Ondo SP Funmilayo Danlami ta tabbatar da lamarin a wata tattaunawa da kafar talabijin ta Channels

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here