Dalilan da suka sa muka gayyaci ICPC bincikar tsarin kudin N-Power – Gwamnatin tarayya

Sadiya Faruq
Sadiya Faruq

Gwamnatin tarayya da Hukumar dakile cin hanci da karbar rashawa ta ICPC sun fara wani yunƙuri don bankado lamuran karkatar da kudade da suka shafi shirin N-Power.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa shirin N-Power wani shiri ne da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa a ranar 8 ga watan Yuni, 2016, domin magance matsalolin rashin aikin yi da matasa ke fuskanta da kuma taimakawa wajen bunkasa zamantakewa.

Wata sanarwa da babban sakatare a ma’aikatar jin kai, Dr Nasir Sani-Gwarzo ya fitar, ta ce an samu sabani iri iri a tsarin biyan masu cin gajiyar N-Power.

Sanarwar ta ce wasu ma’aikatan Hukumar Biyan Kuɗi ne suka aiwatar don haka akwai bukatar a gayyaci hukumar da ke yaki.

Sanarwar ta ce, Sani-Gwarzo ya kuma yi kira ga al’umma da su rika kai rahoton duk wasu kura-kurai da suka faru dangane da shirin ta kowace hanya kamar haka: npowersupport@nsip.gov.ng ko npowerinfo@nsip.gov.ng ko kuma a kira 07030859183.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here