Cibiyar Fasahar Sadarwa da Cigaban Al’umma (CITAD) ta bayyana damuwa kan kamawa da kuma tsarewa ba bisa ƙa’ida ba da aka yi wa Zakariyya Kabeer Gwagwarwa, guda daga cikin ɗan yiwa ƙasa hidima daga jihar Kano da yake yi a jihar Katsina.
A cikin wata sanarwa da Daraktan CITAD, Y. Z. Ya’u ya fitar a ranar Talata, cibiyar ta bayyana cewa rahotanni sun nuna ’yan sanda a Katsina ne suka kama shi bisa umarnin wani ɗan majalisar wakilai na tarayya mai wakiltar mazabar Nassarawa a jihar Kano.
CITAD ta ce laifin da aka ɗora masa kawai shi ne rubutun da ya yi a shafin Facebook da ke cewa: “Kamfani Pampers dole ya tafi Sabuwar Nassarawa a 2027 Insha Allahu.”
Sanarwar ta jaddada cewa wannan rubutu ba zama cin mutunci ko kuma yunkurin da zai taɓa kawo tashin hankali ba, kuma yana cikin ’yancin faɗar albarkacin baki da kundin tsarin mulkin ƙasa ya tabbatar.
Bayan kwanaki da dama a tsare ba tare da samun damar tuntuɓar iyalansa ba, an gurfanar da Zakariyya a gaban kotu, amma maimakon a sake shi, an dage shari’ar na tsawon makonni biyu, abin da CITAD ta kira da tsawaita tsare shi ba bisa ka’ida ba.
Sanarwar ta ƙara da cewa akwai sahihan rahotanni da ke nuna an ci zarafinsa a hannun ’yan sanda, har da suka.
Wannan, a cewar CITAD, abin takaici ne musamman ganin yadda aka ruwaito wani matashin malamin addini daga Dorayi ya rasu kwanan nan a hannun ’yan sanda a tsare.
CITAD ta yi kira da a gaggauta sakin Zakariyya Kabeer Gwagwarwa ba tare da sharadi ba, tare da roƙon kotunan Najeriya da su tabbatar da gaskiya, adalci da ’yanci, su kuma guji zama kayan aiki na tsangwamar siyasa.
Haka kuma ta ja hankalin ’yan sanda da su tuna cewa aikinsu shi ne kare ’yancin ’yan ƙasa, ba amfani da karfi wajen tsoratar da jama’a saboda muradin masu mulki ba.
Ta ce dimokuraɗiyyar Najeriya ba za ta dore ba sai an girmama ’yancin ɗan ƙasa da bin doka, domin kuwa takunkumi kan ’yancin magana, a cewar CITAD, hanya ce ta tura ƙasar ga mulkin kama-karya wanda dole a kauce masa.













































