An ci gaba da yajin aiki bayan tattaunawa tsakanin Dangote, PENGASSAN da gwamnatin tarayya ta tashi ba tare da cimma matsaya ba

PENGASSAN Dangote 860x482 1.jpg 750x430 (2)

Tattaunawar sulhu tsakanin gwamnatin tarayya, ƙungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya (PENGASSAN) da kamfanin Dangote ta ƙare ba tare da samun matsaya ba a daren Litinin.

Taron wanda ya ɗauki fiye da awa tara an kira shi ne domin warware rikicin masana’antu da ya samo asali daga korar ma’aikata sama da 800 a matatar man Dangote.

Ministan ƙwadago da ayyukan yi, Alhaji Muhammad Dingyadi, wanda ya jagoranci taron, ya shaida wa manema labarai da safiyar Talata cewa an samu ci gaba, amma batutuwa biyu ne suka rage a kan teburi da suka hada da batun dawo da ma’aikatan da aka kori da batun ƙungiyoyin ma’aikata.

Shugaban PENGASSAN, Mista Festus Osifo, ya ce ba a cimma matsaya ba kan ma’aikatan da aka kora.

Karanta: Kotu ta hana PENGASSAN da wasu katse ayyukan kamfanin man Dangote

Ya yi gargadi cewa idan ba a maido da su ba, rayuwar sana’o’insu za ta lalace gaba ɗaya, kasancewar an riga an sanya musu lakabin “masu yi wa ƙasa zagon ƙasa” wanda zai hana sauran kamfanoni ɗaukar su aiki.

Osifo ya ƙara da cewa kamfanin Dangote ya amince da batun korar ma’aikatan, inda har wasikun korar suka bayyana a kafafen yaɗa labarai.

Ya ce matsayin ƙungiyarsu a bayyane yake, domin kuwa idan aka dawo da su yanzu, za su dakatar da yajin aiki nan take.

A nasa bangaren, Ministan Kuɗi kuma Ministan tsare-tsaren tattalin Arziki, Mista Wale Edun, ya nuna damuwa kan illar yajin aikin ga tattalin arzikin ƙasa.

Ya ce ya zama dole a kawo ƙarshen rikicin domin kada ya karya ci gaban da aka samu a cikin tattalin arziki, musamman wajen samar da iskar gas da man fetur ga masana’antu.

Ya kuma bayyana cewa gwamnati na da kwarin gwiwar kawo ƙarshen wannan rikici domin a bar tattalin arzikin ƙasa ya ci gaba da tafiya.

Yajin aikin dai zai ci gaba har sai an sake komawa tattaunawa da yammacin yau domin neman mafita.

NAN

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here