Kotu ta hana PENGASSAN da wasu katse ayyukan kamfanin man Dangote

PENGASSAN Dangote 860x482 1.jpg 750x430 (1)

Mai shari’a Emmanuel Subilim na kotun masana’antu ta kasa da ke Abuja ya bayar da umarnin dakatarwa ga kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya (PENGASSAN) daga fara yajin aikin da ta shirya yi kan kamfanin man fetur na Dangote da iskar gas.

Alkalin ya yanke wannan hukunci ne a kan wata bukatar gaggawa da lauyoyin kamfanin Dangote suka shigar.

Wannan ya hada da hana wadanda ake kara – ciki har da kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), hukumar kula da iskar gas da rarraba mai a kasa, da hukumar kula da harkokin hakar man fetur daga dakatar da isar da danyen mai da iskar gas ga kamfanin Dangote.

Lauyan kamfanin George Ibrahim (SAN), shi ne ya jagoranci gabatar da bukatar, inda ya ce kamfanin Dangote yana da lasisin samarwa da rarraba man fetur da kayayyakin sinadarai domin amfani ga al’umma, kuma ayyukansa suna daga cikin muhimmin ɓangare da tattalin arzikin kasa ke bukata.

Ya bayyana cewa a kwanakin baya an samu ayyukan barna daga wasu ma’aikata a masana’antar, lamarin da ya tayar da damuwa kan tsaron rayukan mutane.

Wannan ya sa hukumar kamfanin ta dauki matakin sake fasalin ma’aikata, inda wasu kadan daga cikinsu aka sallama daga aiki, abin da aka sanar ta wata sanarwa a ranar 25 ga Satumba, 2025.

Sai dai Ibrahim ya bayyana cewa a washegari an yada rahoton cewa an kori ma’aikatan ne saboda shiga kungiyar PENGASSAN.

Labari mai alaƙa: PENGASSAN ta dakatar da kai iskar gas zuwa Kamfanin Mai na Dangote

Kamfanin ya karyata wannan batu, inda ya ce ba ya adawa da ma’aikata su shiga kungiya, amma matsalar ta samo asali ne daga lalata kayan aiki da barazanar tsaro.

A cewarsa, shugaban PENGASSAN ya rubuta wasika ga ministan man fetur da iskar gas yana gargadin cewa idan kamfanin bai dawo da ma’aikatan da aka sallama ba, sama da 800 a cewarsu, za su dauki matakin da zai durkusar da kamfanin.

Mai shari’a Subilim a hukuncinsa ya ce ci gaba da yajin aikin zai iya janyo mummunan asara da kuma hana al’umma hidima mai muhimmanci.

Ya kara da cewa, akwai bukatar kotu ta dakatar da wadanda ake kara domin tabbatar da zaman lafiya a masana’antu har zuwa lokacin da za a saurari karar gaba daya.

Kotun ta bayar da umarnin cewa wannan dakatarwa za ta yi aiki na kwanaki bakwai kacal, sannan ta umarci a mika takardun ga wadanda ake kara tare da sanar da su daftarin bukatar da za a saurara a ranar 13 ga Oktoba.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here