Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA Ta hukunta kasar Afrika ta Kudu bisa amfani da dan wasan da bai cancanta ba a wasan neman cancantar buga gasar cin kofin Duniya.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, kwamitin ladabtarwa na hukumar ƙwallon Kafa ta Duniya FIFA ya tabbatar da cewa Afirka ta Kudu ta karya sashe na 19 na dokokin ladabtarwarta da kuma sashe na 14 na ka’idojin gasar cin kofin duniya ta 2026.
Hakan ya faru ne a wasan rukunin da take na C da suka buga da Lesotho a ranar 21 ga watan Maris din, 2025, inda suka saka Tebogo Mokoena duk da rashin cancantarsa.
Saboda haka, Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA ta ba Lesotho nasara da ci 3-0, sannan ta rage wa Afirka ta Kudu maki 3 inda yanzu ya zamana tana da maki 14 mai makon 17 da take dashi a baya hakan ya sa ta sauka daga matakin da take na 1 zuwa na 2 a rukunin da take.
Wannan hukunci ya bai wa kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles damar samun cancantar zuwa gasar, amma fa sai idan Benin ko Afrika ta Kudu da suke da maki 14 kowannen su sun yi rashin nasara a wasanni biyun da suka rage musu ita kuma Najeriya ta ci dukkan wasannin nata.
Sai dai kuma, har yanzu wannan hukunci yana da damar daukaka kara a gaban kwamitin daukaka kara na Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA.
Ga yadda jadawalin rukunin na C yake:
Benin – Maki 14 ( Tazarar kwallaye 4)
Afirka ta Kudu – Maki 14 ( Tazarar kwallaye 3 )
Najeriya – Maki 11 ( Tazarar kwallaye )
Rwanda – Maki 11 ( Babu tazarar kwallo ko daya)
Lesotho – Maki 9 ( Ana binta bashin kwallaye 3)
Zimbabwe – Maki 4













































