Tsohon mataimakin gwamnan jihar Edo, Comrade Phillip Shaibu, ya caccaki yadda NFF ta raba gari da Finidi George a matsayin kocin Super Eagles.
Da yake jawabi bayan shi, a matsayinsa na bako, kyaftin din kungiyar ‘yan jarida a gasar NUJ da ke gudana, Kwamared Shaibu ya ce hakuri kadan zai iya daidaita al’amura.
“A gare ni da zan bar Finidi George don ci gaba da kungiyar, in ba shi lokaci don gina kungiyar,” in ji tsohon gwamnan wanda kuma ya taka leda a matsayin memba na Inshora FC.
Karin labari: Majalisar wakilan Najeriya ta shiga maganar hukumar PSC da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda
“Na sami irin wannan matsala lokacin da muka yanke shawarar sake gina Bendel Insurance FC. Akwai matsin lamba daga mutane da yawa su kori kocin, amma na zabi ban yi ba.
“Maimakon haka, mun kawo wasu ‘yan wasa kuma bayan shekaru uku, mun ci nasara zuwa NPFL, ba a doke mu a kakar wasa ba sannan kuma muka ci kofin FA bayan shekaru 43.”
Karin labari: Wata motar man fetur ta kama da wuta a gidan man Mainland a Abuja
Kwamared Shaibu ya kara da cewa: “Muna bukatar hakuri don samun nasara, kun san duk ‘yan Najeriya koci ne. Idan ka kawo bature ya zama kocin Super Eagles, bambancin launi ne kawai, ina ganin muna da abin da ake bukata a nan, wannan shi ne ra’ayina.”
Finidi George ya yi murabus a matsayin kocin Super Eagles kasa da watanni biyu da aiki.
Hakan ya zo ne a daidai lokacin da NFF ke shirin daukar mai ba da shawara kan fasaha wanda zai maye gurbinsa.